Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, ya yi kira da a samar da karin asibitoci masu zaman kansu, domin su taimaka wajen inganta harkar lafiya a jihar. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da wani asibiti mai zaman kan shi mai suna ‘Foresight Premier Hospitals,” wanda wani dan jihar, Dokta Shamsu Aliyu ya kafa.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Ya Kai Ziyara Bata Aiki A Asibitin Jahar Sokoto
Gwamnan wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba wa wanda ya kirkiro da hangen nesa, sannan ya bukaci sauran masu kishin jihar da su yi koyi da shi.
Wamakko ya ce samar da asibitoci masu zaman kansu a jihar zai kara kusantar da harkokin kiwon lafiya ga jama’a. Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba da kulawa ga asibitin domin samun kwarin gwiwar samar da karin cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar.
Wamakko, ya tabbatar da cewa ya kuma gina wani asibiti mai zaman kansa a jihar, wanda nan ba da dadewa ba za a kaddamar da shi a wani bangare na kokarin samar da ingantaccen kiwon lafiya.
Ya kuma yaba wa Dokta Mansur Isah Buhari da Dr. Bashir Muhammad Achida daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato bisa irin rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan sanin hakkinsu a kowane lokaci.
Da yake jawabi tun da farko, wanda ya kafa cibiyar kiwon lafiya, Dakta Aliyu, ya bayyana cewa ana shirin samar da karin asibitoci a shiyyar da ma kasa baki daya. Ya ce wannan ita ce hanyarsa ta kawo tallafi ga marasa galihu a jihar.
A nasa bangaren, Dakta Buhari, ya bayyana cibiyar kiwon lafiya a matsayin wani babban asibiti mai inganci na zamani, wanda ke da kayan aiki na zamani. Ya yi bayanin cewa asibitin mai gadaje 24 yana da dakin tiyata, kantin magani, dakin aiki, sashin kula da marasa lafiya, dakunan kwana maza da mata, da dakin warkewa, da dai sauran kayayyakin da ake bukata asibiti ya yi tasiri. Wannan a cewarsa, zai samar da ayyukan yi kusan 300 ga al’ummar jihar.
Leave a Reply