Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), don kammala wa’adinsa.
Ku tuna cewa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barr Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.
Karanta Haka: Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Sai dai wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta ce mayar da aikin na nan take tare da bin umarnin kotu.
Karanta kuma: Gwamnan Kano ya nada mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.
LN.
Leave a Reply