Take a fresh look at your lifestyle.

Kotun Daukaka Kara Ta Dawo Da Tsohon Shugaban Hukumar NIA Mohammed Dauda

0 134

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta mayar da tsohon Darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa NIA Mohammed Dauda bakin aiki.

 

Da yake yanke hukunci a yammacin ranar Alhamis, Mai shari’a Peter Ige ya ce, shaidun da suka kai ga korar Dauda ba su da tushe balle makama.

 

Kotun ta Appallet ta kuma warware duk wasu batutuwan da suka taso a kan NIA a madadin Dauda wanda shi ne wanda ake kara a karar.

 

Kotun ta bayar da umarnin a biya Dauda albashi da hakkokinsa tun ranar da aka kore shi daga aiki.

 

Kotun daukaka kara ta kuma bayar da umarnin a biya Dauda kudaden da suka kai Naira miliyan daya.

 

Mai shari’a Ige ya ci gaba da cewa, “Ya kamata a bar Dauda ya yi ritaya daga aiki bisa ga dokokin da aka gindaya.

 

Kotun ta ce: “Babu wata shaida da ke gaban kotu da ke nuna cewa wanda ake kara ya yi kasada ko kuma ya keta wata doka.”

 

Mai shari’a Ige ya ce “An yi watsi da karar saboda rashin cancanta kuma an tabbatar da hukuncin kotun masana’antu.”

 

Idan dai za a iya tunawa, tsohon Darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa NIA Mohammed Dauda ya rike mukamin shugaban hukumar tsaro ta Najeriya daga watan Nuwamba 2017 zuwa Janairun 2018, inda ya maye gurbin shi da mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Dauda ya shafe watanni kadan yana aikin kafin a cire shi.

 

Da yake rashin gamsuwa da tsige shi da aka yi ba bisa ka’ida ba, Dauda ya kalubalanci tsige shi a gaban kotu, inda ya ce korar sa daga aiki ba ta bi ka’ida ba kuma kuskure ne.

 

Ya kara da cewa, wanda ya saba wa doka, babu wani jami’in gudanarwa na musamman na kwamitin ladabtarwa (SMSDC) da aka kafa domin binciken tuhume-tuhumen da ake yi masa, kuma ba a yi masa adalci ba bayan haka.

 

A wani hukuncin farko da mai shari’a Olufunke Anuwe, na kotun masana’antu ya yanke, ya bayar da umarnin mayar da Mohammed Dauda a matsayin shugaban hukumar leken asiri ta kasa tare da biyan albashi da hakkokinsu daga watan Maris na 2018 zuwa yau bayan ta gano cewa korar tasa ta yi kasa a gwiwa.

 

An yanke hukuncin cewa “a karkashin dokar hukumar, kwamitin da ya dace ya binciki shari’ar ladabtarwa ga ma’aikatan gudanarwa shine kwamitin ladabtar da ma’aikatan gudanarwa, “ba kwamitin ladabtarwa na ma’aikatan gudanarwa na musamman ba.”

 

LN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *