Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar JAMB Ta Amince Rage Maki 140 Domin Samun Shiga Jami’o’i

0 103

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya maki 140 zuwa sama da haka a matsayin makin da za a yanke na shekarar 2023 don shiga jami’o’in kasar nan.

 

 

Magatakardar hukumar Farfesa Is-haq Oloyede ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron siyasa na shekarar 2023 kan shiga manyan makarantu da bayar da kyaututtuka da aka yi ranar Asabar a Abuja.

 

 

Oloyede ya ce an amince da 100 a matsayin makin da za a yanke wa Makarantun Kimiyya da Kwalejojin Ilimi.

 

 

Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa abubuwan da aka ambata sune mafi karanci, amma hakan ba yana nufin dole ne hukumomi su bi su ba.

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *