A ranar Alhamis ne D’Tigers ta Najeriya ta isa birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire domin buga gasar FIBA ta shiyyar Afirka ta 3 da za a fara yau a filin wasa na Palais des Sports de Treichville.
KU KARANTA: Ghana za ta karbi bakuncin gasar FIBA U16 ta 2023
Kungiyar da ta fi rinjaye ‘yan wasan gida ta samu jagorancin koci Ogoh Odaudu kuma da idon su kan tikitin shiga gasar.
Za a yi wasannin share fage ne daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli, inda D’Tigers za ta kara da Guinea a wasansu na farko ranar Juma’a.
Za su kara da Jamhuriyar Benin a ranar Asabar kafin su kara da Ivory Coast a wasan karshe a ranar Lahadi.
Wanda ya yi nasara a wasannin share fage na karshen wannan makon zai hadu da Kenya da Gabon a rukunin A na FIBA AfroCan na 2023 da ke gudana a Angola daga 8-16 ga Yuli 2023.
Jerin Sunaye:
Johnson Anaiye, Okiki Micheal, Victor Ezeh, Micheal Daramola, Odufuwa Kanyinsola, Wisdom Anyoaha, Ibe Agu, Victor Koko, Chinedu Chimbou, Tolani Buhari, Abba Adamu, Adebayo Oduleye.
L.N
Leave a Reply