Take a fresh look at your lifestyle.

Libya: jiragen yaki mara matuki ya kai wa sansanin Wagner hari- Sojoji

0 133

Harin da jiragen yaki mara matuki da ba a san ko su waye ba a daren ranar Alhamis din da ta gabata sun kai hari a wani sansanin sojin sama da ke gabashin Libya inda ake kyautata zaton sojojin hayar kungiyar Wagner ta Rasha ta girke, ba tare da haddasa hasarar rayuka ba a cewar wata majiyar soji.

 

Majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa jiragen da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a sansanin sojin sama na al-Kharrouba, mai tazarar kilomita 150 kudu maso gabas da Benghazi (gabas), inda ake kyautata zaton akwai wasu gungun ‘yan kungiyar Wagner.

 

“Hare-haren ba su haifar da asarar rai ba”, in ji ta.

 

Kasar Libya dai ta fada cikin wani babban rikicin siyasa tun bayan hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, wanda ya ruguza sakamakon rarrabuwar kawuna tsakanin gabashi da yamma da kuma tsoma bakin kasashen waje.

 

Daga Afrilu 2019 zuwa Yuni 2020, Khalifa Haftar, mai karfi a gabashin Libya, ya yi amfani da mayakan Chadi, Sudan, Najeriya da Siriya, amma sama da duk sojojin haya daga Wagner, a yunkurinsa na kwace Tripoli babban birnin kasar.

 

Tun daga wannan lokacin ne daruruwan ‘yan kungiyar Wagner ke ci gaba da gudanar da ayyukansu a gabashi, a yankin da ake da man fetur, da kuma kudancin Libya bayan da wasu sojojinsu suka tashi zuwa Mali ko Ukraine domin yaki tare da sojojin Rasha.

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *