Wata motar bas ta yi hatsari tare da kone kurmus, inda ta kashe mutane akalla 25 a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya, kamar yadda ‘yan sanda da jami’ai suka bayyana.
“Bas din na tafiya ne daga Nagpur zuwa Pune a lokacin da misalin karfe 1:35 na safe ta hadu da wani hadari a kan titin Samruddhi Mahamarg, bayan da tankar dizal ta bas din ta kama wuta,” in ji ‘yan sandan yankin.
“Yawancin mace-mace sun faru ne saboda konewa.”
Mutane 25 ne suka mutu sannan takwas suka jikkata, mataimakin babban ministan Maharashtra Devendra Fadnavis ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter.
Babban Ministan jihar Eknath Shinde da Firayim Minista Narendra Modi sun buga a shafin twitter daban-daban suna nuna bakin ciki kuma sun ce za su biya tallafi ga dangin kowane da abin ya shafa, wanda ya kai kudin Indiya 700,000 ($ 8,500).
L.N
Leave a Reply