Gwamnatin Jihar Osun Za Ta Samar Da Ofishin ‘Yan Najeriya MaZauna Kasashen Waje
Gwamnatin jihar Osun dake kudu maso yammacin Najeriya na shirin kafa ofishin ‘yan kasashen waje.
Ofishin zai biya bukatun ’yan asalin jihar Osun a kasashen Afirka da dama da sauran sassan duniya.
Gwamnan jihar, Ademola Adeleke, yayin da ya karbi bakuncin ‘yan asalin jihar Osun da suka zo bikin Sallah daga kasashen waje ya bayyana hakan.
Ya ce: “Ku gaya wa mutanenmu daga Cotonou zuwa Abidjan, daga Landan zuwa Atlanta cewa muna da shirye-shiryen shigar da su cikin ajandar shugabanci nagari. Ina aiki kan samar da ofishi na kasashen waje don tattara bayanai, shiga da kuma shigar da mutanenmu.
“Na san mutanenmu a fadin Afirka ta Yamma galibi masu sana’a ne da kuma kananan ‘yan kasuwa. Ofishin da aka tsara zai ɗauki bayanan su don ganin inda za su shiga don taimaka musu da tallafa musu. Zan iya nada jami’in hulda da zai kasance a Abidjan.”
Gwamnan wanda ya lura cewa al’ummomin kasashen waje wakilai ne na ci gaba, ya jaddada burin gwamnatinsa na yin amfani da abubuwan da suka dace na wannan al’umma mai mahimmanci.
A cewarsa, baya ga kiyasin dubban daruruwan ‘yan asalin Osun da ke zaune a Benin, Togo, Ghana da kuma masu yawan gaske a Ivory Coast, wadanda ke Turai da Arewacin Amurka za su kasance da hannu.
Ya ce: “Ga al’ummarmu mazauna Arewacin Amurka da Turai, ina cikin ku. Yawan ku ya bambanta da na ’yan’uwanmu da ke yammacin Afirka. Mun riga mun tuntuɓar ku, don fitar da saka hannun jari a cikin Osun kuma mu tabbatar da shigar ku cikin gwamnatinmu.
“Na san wasu garuruwan Osun inda kusan kowane gida yana da ’yan uwa da yawa, na tsararraki da dama a Abidjan, Cotonou da sauransu. Ina so in samar da tsari na yau da kullun don magance wadannan nau’o’in mutanenmu daban-daban”, in ji Gwamnan.
Gwamna Adeleke ya yi alkawarin bayyana cikakken shirin nan da wani lokaci yana mai nuni da cewa Osun na bukatar dukkan hannaye da su tashi tsaye wajen magance kalubalen ci gabanta, da magance talauci da kuma ci gaba cikin sauri.
L.N
Leave a Reply