Sama da ’yan wasa 100 daga sassan Najeriya da wasu kasashe makwabta ne ake sa ran za su fafata a gasar Taekwondo ta Sufeto Janar na ’yan sanda karo na 10 da za a yi a filin wasa na Samson Siasia da ke Yenagoa a Jihar Bayelsa.
Kungiyar ta bayyana cewa gasar da za a yi daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Agusta wata hanya ce da ake amfani da ita wajen gano karin taurari. Akwai nau’o’in shekaru daban-daban da nau’ikan wasanni daban-daban na fama.
KU KARANTA : Kungiyar Taekwondo ta jihar Bayelsa ta lashe gasar cin kofin shugaban kasa na 2023
Da take jawabi gabanin taron, shugabar kungiyar ‘yan sandan taekwondo ta Najeriya (NIPOTA), CSP Stella Ebikefe, ta ce gasar ta bana za ta fi armashi, domin ‘yan wasa da kungiyoyi da dama sun nuna sha’awarsu a gasar.
“Dukkan yankin ‘yan sanda daga shiyya ta 1 zuwa shiyya ta 16, kungiyoyin jahohi 36, kasashe makwabta irin su Benin da Nijar da yara daga shekara biyar da ‘yan wasan Para za su shiga gasar.
“Gasar tana da nufin inganta wasan taekwondo a Najeriya da kuma gano hazikan masu shekaru daban-daban,” in ji ta.
Ta bayyana cewa za a horar da kwararrun kwararrun da aka gano a gasar tare da bayyana su a gasar cikin gida da na kasa da kasa domin bunkasa kwarewarsu.
L.N
Leave a Reply