Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Dakatar Da Karin Kudin Maranta Da Jami’oin Tarayya Suka Yi

Abdulkarim Rabiu

0 167

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC, da ta gaggauta dakatar da aiwatar da karin kudaden makaranta da Jami’o’in Tarayya a fadin kasar suka yi.

Majalisar ta kuma umarci kwamitin kula da manyan makarantu da ayyuka (idan an Kafa shi) ya binciki lamarin, da nufin samar da dawwamammen mafita kan kalubalen da ake fuskanta a bangaren ilimi.

Hakan ya biyo bayan kudirin da dan Mataimakin Shugaban marasa rinjaye, Hon. Aliyu Madaki ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talatar nan.

Dan majalisar wanda har ila yau shi ne ke wakiltar mazabar Dala daga Jihar Kano, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu jam’oin Tarayya a fadin kasar suka kara kudaden adaidai lokacin da talauci ke kara ta’azzara, da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da kuma hauhawar farashin man fetur a baya-bayan nan.

Hon. Madaki ya lura cewa karin da aka yi zai iya haifar da cikas ga dimbin daliban da ba za su iya biyan kudaden ba, yana mai cewa yayin da, da yawa daga cikinsu za a tilasta musu dakatar da karatunsu, wasu Kuma na iya daina karatun baki dayansa.

A cewarsa, Karin kudin na iya kara dagula al’amura da dama a kasar ganin yadda dalibai suka riga suka fara barazanar da ka iya haifar da tayar da kayar baya ga Gwamnatin Tarayya, wanda hakan kan iya haifar da mummunan
sakamakon ga kasa baki daya.

Har ila yau, dan Majalisar ya bayyana fargabar cewa karuwar yawan dalibai dake barin jami’o’i na iya kara ta’azzara tabarbarewar tsaro a Najeriya saboda takaicin daliban na iya sa su bin hanyoyin da ba su dace ba don bayyana kokensu.

Ya kara da cewa ilimin manyan makarantu na da matukar muhimmanci wajen bunkasa ci gaba, rage radadin talauci, da kara habaka wadatar kowace kasa.

Abdulkarim Rabiu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *