Tu’amulli da miyagun ƙwayoyi da ke zama ƙarfen ƙafa a tsakanin al’umma a faɗin duniya wanda kuma ya zama wajibi a yi mai yiyyuwa wajen kawo ƙarshensa ta hanyaki da wannan mummunar ɗabi’ar domin samar da al’umma ta Gari, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin ta NDLEA ita ce aka dorawa alhakin hakan a Najeriya.
A kokarinta na tabbatar da hakan, rundunar hukumar ta shiyar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya ta gudanar da bukin kona kimanin tan 25 na kayan shaye-shaye a gaban bainar jama’a.
Malam Adamu Iro Muhammad shi ne babban kwamandan rundunar na shiyar Sokoto.
“Umurnin Kotu shine ya bamu damar kone kayan mayen wanda ya saɓa zargin da wasu ɓata gari ke yi na cewa wai idan mun kama irin wadannan kwayoyi samar wa mu ke yi wanda hakan ba gaskiya ba ne” in ji Adamu Iro
Da yake magantuwa wajen bukin shugaban hukumar Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai murabus wanda daraktar shara’a ta hukumar ta wakilta ya ce cikin watanni 29 sun samu nasarar chafke wasu gigga-giggan Dillan ƙwayoyin 35 da wasu dubu 32.
Gwamnatin jihar Sokoto ta sha alwashin baiwa hukumar duk irin goyon bayan da ta ke buƙata domin kawar da wannan mummunar ɗabi’ar a ƙasa baki ɗaya.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply