Take a fresh look at your lifestyle.

Gobarar Daji Ta Haddasa Kwashe Mutane A Spain

0 166

Gobarar dajin da ta tashi a tsibirin La Palma da ke Spain ta tilasta kwashe mutane akalla 500, kamar yadda hukumomi suka ce.

 

Rahoton ya ce wannan ne karon farko da ake fama da rikici a tsibirin tun bayan wani aman wuta da aka yi a shekarar 2021.

 

Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar yau a El Pinar de Puntagorda, wani yanki mai dazuzzuka a arewacin tsibirin Canaries, yayin da yawancin biranen Turai ke nuna tsananin zafi a cikin mako mai zuwa.

 

Rahoton ya ce akalla gidaje 11 ne suka lalace yayin da gobarar ta ci gaba, inji shugaban tsibirin Canary, Fernando Clavijo.

 

“Yawancin mutanen da za a kwashe na iya kaiwa 1,000. Ya danganta ne ko za mu iya sarrafa wadannan iska mai karfi,” Clavijo ya shaida wa manema labarai.

 

Ya kara da cewa, kimanin hekta 140 ne gobarar ta lalata.

 

A halin da ake ciki kuma, jirage masu saukar ungulu da jami’an kashe gobara hudu a kasa suna fafatawa don shawo kan wutar da ta tashi a tsibirin, wanda ke zama wani yanki na tsibiran Spain da ke gabar tekun yammacin Afirka.

 

Hukumomin tsibirin suna neman taimako daga wasu tsibiran dake cikin tsibiran, kamar Gomera da Tenerife.

 

A cikin Satumba 2021, fiye da gine-gine 2,000 ne aka lalata kuma an tilastawa dubban mutane barin gidajensu lokacin da lava ya fara kwarara daga dutsen Cumbre Vieja.

 

Fashewar ta ci gaba har na tsawon wata uku sannan tokar lafa ta lullube yankin da bargon bakar kura mai kauri.

 

 

REUTERS/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *