Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Rashin Kammala Aikin Hanyar Kano – Maiduguri
Abdulkarim Rabiu, Abuja
Majalisar wakilan Najeriya za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin abin dake haifar da tsaiko wajen kammala aikin tagwayen titin Kano Zuwa Maiduguri.
Matakin ya biyo bayan wani kudiri da Hon Shitu Galambi daga Jihar Jigawa ya gabatar domin gudanar binciken tare da daukar matakin kammala aikin, a zaman Majalisar na ranar Talatar nan.
Da yake gabatar da kudirin Hon Yusuf Shittu Galambi ya bayyana cewa tun a shekara ta 2006 gwamnatin tarayyar ta bada kwantiragin aikin tagwayen hanyar Kuma aka Kasa shi gida 5, Inda kashin farko na aikin mai nisan kilomita 202 ya kunshi garuruwan kano, Wudil da Gaya daga Jihar Kano da Kuma Shuwarin a cikin Jihar jigawa.
Ya ce Kamfanin Dantata & Sawo aka baiwa kwantiragin kashin farko na aikin hanyar wanda ba a kammala ba yayin da Kawo yanzu an riga an kammala sauran Kashi hudu na aikin hanyar.
Dan Majalisar ya Kuma bayyana damuwarsa kan yadda aka yi watsi da aikin ba tare da wani kwakkwaran bayani duk kuwa kudin da gwamnatin tarayya ta ware domin gudanar da aikin.
Har ila yau ya nuna damuwarsa dangane yadda ake samun haddura akai akai sakamon rashin kyawun hanyar sannan batagari na anfani da damar wajen aikata ba daidai ba akan matafiya.
Ya Kara da cewa rashin kyawun hanyar ya haifan da koma bayan tattalin arziki Inda ya bayyana cewa kammala aiki zai taimaka wajen samar da tsaro ga matafiya da bunkasa tattalin arzikin al’umomonin dake zaune a yankin.
Da take yanke shawara kan kudirin Majalisar ta ce zata Kafa kwamiti na musanman domin gudanar da bincike akan musabbabin rashin kammala aikin tare tabbatar da Magance matsaloliin dake Kawo cikas don kammala aikin kana ya gabatar da rahoto cikin makwanni uku.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply