Take a fresh look at your lifestyle.

YAN SIYASA A JIHAR KOGI SUN YI KUDIRI SAMAR DA KURI’U MILIYAN DAYA

Daga Aanya Igomu

0 223

Gamayyar kungiyoyin tsofaffin masu rike da mukaman siyasa a jihar Kogi, sun ce sun kudiri aniyar samar da akalla kuri’u miliyan daya ga Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Sanata Bola Tinubu a zabe mai zuwa a Najeriya.

Gamayyar wadanda suka rike mukaman siyasa a baya, tun daga gwamnan jihar Kogi na farko har zuwa lokacin da ake gudanar da siyasa a yanzu, su ne masu wayar da kan jama’a.

Shugaban kungiyar, Abdulmumin Sadik, ya shaidawa manema labarai a Abuja. Ya ce, a matsayinsu na ‘yan siyasa na gari suna da karfin kawo kuri’u.

“Wadannan mutanen grass root mobilisers ne a kananan hukumomi ashirin da daya. Haka nan muna da jama’a a gundumomi tun daga mazabu har zuwa rumfunan zabe kuma muna da niyyar tabbatar da cewa mun samar da kuri’u da bai gaza dari biyu ba daga kowace rumfar zabe, har zuwa unguwa da karamar hukuma. Idan kuka tattara duka wadannan kuri’u, hakan na nufin ba za ku samu kuri’u kasa da miliyan daya ga mai girma Ahmed Bola Tinubu ba a zabe mai zuwa,” in ji Sadik.

Ya ce kungiyar na da cikakken goyon bayan Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Shugaban gamayyar ya kuma yi jawabi a kan ko Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi na barazana ga Dan takarar jam’iyyar APC, ganin cewa sun fitar da tikitin tsayawa takara tsakanin musulmi da musulmi.

Sadik, yayin da yake yaba wa halayen Mista Obi, ya ce Dan takarar jam’iyyar Labour, yana cikin takara a lokacin da bai dace ba.

“Ba za ku iya kwatanta Peter Obi da Bola Ahmed Tinubu ba, saboda maki a bayyane yake. Jihar Legas, tamkar hada dukkan jihohin Kudu maso Gabas ne, a matsayin jiha daya ga jihar Legas. Tattalin arzikin jihar Legas tamkar hada tattalin arzikin jihohin Kudu maso Gabas ne ga jihar Legas.

Idan Tinubu zai iya sauya tattalin arzikin jihar Legas, ga abin da ya yi a cikin shekaru takwas ba za ka kwatanta da abin da Peter Obi, ya yi a jiharsa tsawon shekaru takwas. Don haka Tinubu yana da tarihin da kowa zai iya gani kuma wannan rikodin ya yi daidai. A wurina  Peter Obi,  yana da nasa halaye amma ina ganin a yanzu yana kasuwa a lokacin da bai dace ba, saboda yana da Dan takara a APC wanda ya fi shi cancanta,” inji shi.

Mista Sadik, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su maida hankali wajen zabar shugabanni bisa cancanta maimakon addini.

“Ya kara da cewa, dole ne mu ga yadda za a sake dawo da kasar nan daga cikin manyan tarnaki guda uku, kabilanci, addini da aji kuma idan ka duba, talauci bai san kai Musulmi ne ko Kirista ba, rashin tsaro bai san Musulmi ba. ko Kirista, duk alkaluman da ke ci mana tuwo a kwarya a kasar a yau, ba su da alaka da kai Musulmi ne ko Kirista,”

 

 

AISHA YAHAYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *