Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta karbi bakuncin takwararta ta Japan.
Taron ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwa tsakanin Pretoria da Tokyo. Japan na ɗaya daga cikin manyan masu saka hannun jari a Afirka ta Kudu,” in ji Naledi Pandor.
“Kasarmu ta amince da goyon bayan da jama’a da gwamnatin Japan suka ba mu. Mun kuma fahimci irin rawar da kamfanonin Japan suka taka wajen tallafawa tattalin arzikinmu da masana’antu a Afirka ta Kudu,” in ji ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu.
Tare da wasu kamfanoni 273 na Japan da ke aiki a Afirka ta Kudu, suna samar da ayyuka sama da 200,000, shugaban diflomasiyyar Japan ya yi kira da a kara yin hadin gwiwa da Pretoria.
Hayashi zai yi amfani da rangadin da ya yi a Afirka don jaddada mahimmancin sabunta yarjejeniyar hatsin da aka kulla a tekun Black Sea.
Yarjejeniyar ta shafi jigilar hatsi ba kawai zuwa Afirka ba amma zuwa Asiya da Turai, kuma tana da babban tasiri ga sarkar samar da abinci a duniya.
Maimuna Kassim Tukur
Leave a Reply