Take a fresh look at your lifestyle.

Cire Tallafi: Kungiyoyin Kwadago na Jihar Ebonyi Sun Shiga Zanga-zangar Lami Lafiya

0 86

Kungiyar Kwadago a jihar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jaha da su ba da fifiko wajen rage kudin gudanar da mulki domin samun ci gaba mai dorewa.

 

Kungiyoyin da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma Trade Union Congress of Nigeria (TUC), sun yi nuni da cewa irin wannan matakin zai taimaka matuka wajen adana karin kudade ga gwamnati don magance bukatun jama’a.

 

Sun bayyana hakan ne a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a ranar Larabar da ta gabata, a yayin zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.

 

Muryar Najeriya ta tattaro cewa kungiyoyin sun kuma bukaci karin mafi karancin albashi na kasa daga N30,000 zuwa N200,000.

 

Farfesa Oguguo Egwu, Shugaban NLC a Ebonyi ya ce zanga-zangar lumana ita ce aikewa da sako a hukumance ga masu mulki kan bukatar yin amfani da abubuwan da suka shafi jin dadin ma’aikata.

 

A cewar Egwu, zanga-zangar ba wai ga wani mutum bane illa aikewa da sako ga shugabannin.

 

“Ba wai zanga-zangar nuna adawa da kowane mutum bane illa zanga-zangar adawa da zaluncin masu mulki wanda ya jefa ma’aikata cikin rashin daidaiton tattalin arziki. Ya kamata a yi la’akari da rage hawan man fetur, rage kudin makaranta da duk wani nau’i na kara kuzari don ciyar da al’umma gaba.

 

“Sa matatun man mu su yi aiki, su baiwa talakawa ma’aikata damar samun ilimi a kan farashi mai rahusa.

 

 “Ma’aikata suna kuka, muna bukatar albashin mu saboda mafi karancin albashi ba zai iya ci gaba da daukar mu ba,” in ji Shugaban NLC.

 

Shima da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar TUC a jihar, Comrade Chidi Igboji, ya koka kan yadda ‘yan kasar ke fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin.

 

Igboji ya sake yin kira ga bukatar rage kudaden tafiyar da gwamnati domin amfanin talakawan kasa.

 

Muryar Najeriya ta kara tattaro cewa an rufe dukkan bankunan jihar saboda zanga-zangar.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *