Take a fresh look at your lifestyle.

NAJERIYA NA KASHE TALLAFIN BILIYON N18.397b A KULLUM– MINISTA

THERESA ZUGWAI PETER

0 212

Ministar kudi, watu malama zainab Ahmed, ta ce Najeriya na kashe naira biliyan 18.69 a kullum kan tallafin man fetur.

 

Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke a gaban kwamitin gida na majalisar wakilai da aka yi daga shekarar 2013 zuwa 2021, biyo bayan kira da aka yi.

 

Ta ce, akwai kwamitin da shugaban kasa  ya  kafa  na sa ido kan kudaden shiga, wanda ma’aikatar ta jagoranta, domin daidaita kudaden shigar da ake samu, hukumomi su rika fitar da duk wani kudin da ba za a iya turawa ba.

 

Shagaban kwamitin wucin gadi, Ibrahim Aliyu ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin binken inganci ko akasin haka na tsarin tallafin.

 

Aliyu ya bayana damuwarsa kan kalaman da ministan kudi ya yi a baya baya nan na cewa kasar na bukatar tallafin naira tiriliyan 6.7 a shekarar 2023.

 

Sai dai kwamitin ya gayyaci Akanta janar na tarayya da ya gurfana a gabansa a ranar 25 ga wannan wata domin amsa wasu batutuwa da aka tabo.

Theresa zugwai peter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *