Magajin garin London zai ba da kwarin guiwa ga duk direbobin da za su kwashe tsofaffin motocin dake anfani da man fetur ko dizal a wani yunkuri na kwantar da tarzoma kan shirin tsaftar yanayi wanda ya matsa lamba ga jam’iyyar adawa ta Labour kafin zaben kasa da ake sa ran za a yi a shekara mai zuwa.
Gabanin shirin fadada yankin Ultra Low Emission, Sadiq Khan ya ce a yanzu za a bayar da tallafin kudi na ababen hawa a fadin hukumar, kuma ba wai kawai domin mutane masu karamin karfi ko nakasassu ko kananan sana’o’i ba.
“Na ci gaba da sauraron damuwar ‘yan London a cikin ‘yan watannin nan.
Kowane dan London da ke da motar da ba ta dace da ULEZ ba, yanzu za ta cancanci tallafin kuɗi, “in ji Khan a cikin wata sanarwa.
Yanzu za a bayar da tallafin fam 2,000 ga kowa da kowa kuma za a kara yawan kudaden da ake kashewa ga kungiyoyin agaji, kasuwanci da sauran su.
Khan yana shirin tsawaita ULEZ don rufe kusan dukkanin babban birnin Landan, wanda zai kunshi karin mutane miliyan biyar a gundumomin waje, daga ranar 29 ga Agusta.
Majalisar City ta kiyasta kashi 90% na motoci a wajen Landan sun riga sun yarda da ULEZ. Masu adawa sun kalubalanci wannan adadi
Bayan sakamakon zaben da aka gudanar a watan Yuli, shugaban jam’iyyar Labour Keir Starmer ya fito fili ya nemi Khan ya yi tunani kan dalilin da ya sa jam’iyyar ba ta lashe kujerar majalisar ba.
Labour tana da jagorar kusan kashi 20 cikin dari akan masu ra’ayin mazan jiya na Firayim Minista Rishi Sunak. Ana sa ran Sunak zai kira zaben kasa kafin karshen 2024.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply