Take a fresh look at your lifestyle.

Isra’ila ta kwashe Yahudawa daga yankunan da ake rikici a Habasha

0 117

Isra’ila ta sanar da cewa ta kwashe sama da ‘yan kasarta 200 a cikin wani jirgin sama na musamman daga garuruwa biyu na yankunan Amhara da Oromia da rikicin baya-bayan nan ya shafa tare da kai su Addis Ababa babban birnin kasar.

 

Yankin Amhara na da dubban mabiya al’ummar Yahudawa.

 

A cikin wata sanarwa da Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya fitar ya ce ya ba da umarnin a kwashe mutanen daga yankunan da ake gwabzawa kuma za su tashi zuwa Isra’ila.

 

Ana ci gaba da samun kwanciyar hankali a manyan biranen yankin Amhara a daidai lokacin da ake gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da mayakan sa-kai na yankin.

 

Sojojin kasar sun ce sun sake samun iko a wasu yankuna masu muhimmanci amma mazauna wasu kananan garuruwa da yankunan karkara sun ce har yanzu mayakan sa kai na yankin ne ke da iko.

 

A halin da ake ciki Amurka da Birtaniya sun hada hannu da wasu kasashe uku – Japan, Australia da New Zealand – don nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Habasha.

 

Wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a ranar Juma’a ta ce tashin hankalin baya bayan nan a yankunan Amhara da Oromia na kasar “sun yi sanadin mutuwar fararen hula da rashin zaman lafiya”.

 

 

Hukumar kula da kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Habasha tun da farko ta ce ta damu matuka dangane da rashin tsaro na baya-bayan nan, kuma ta yi kira ga gwamnati da ta bi ka’idojin wajibci, daidaito, da rashin nuna wariya’ wajen aiwatar da dokar ta baci da aka ayyana a kasar. alaka da tashin hankali.

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *