Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya ya kaddamar da rabon kayan abinci da kayan aikin noma a matsayin agajin gaggawa domin rage wahalhalun da tattalin arzikin kasa ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.
Wannan matakin ya shafi masu cin gajiyar 30,000 inda kowannensu ya tattara buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 5, katon taliya daya, buhunan taki biyu, da lita biyu na maganin kashe kwari.
A yayin bikin raba kayayyakin a fadar Sarkin Yamaltu da ke yankin Dadinkowa a jihar, Gwamna Yahaya ya ce; “Kaddamar da rabon kayan tallafin wani gagarumin yunƙuri ne da nufin taimakawa sama da masu cin gajiyar 450,000 a duk ƙananan hukumomi 11 na jihar.”
Ya ce rabon tallafin na yanzu ya kasance na musamman domin ya hada da kayan noma kuma ya yi matukar farin ciki da gaskiyar cewa kaso mai tsoka na al’ummar Gombe sun dogara ne kan noma don rayuwarsu.
“Samar da tallafin noma ba wai kawai yana tabbatar da girbi mai yawa ba, har ma yana ƙarfafa samar da abinci, musamman a lokacin rani mai zuwa,” in ji Gwamna Yahaya.
Ya bayyana cewa, wannan tallafin wani mataki ne na tabbatar da dorewar tattalin arzikin kasa da kuma samun ci gaba bisa la’akari da illolin kalubale iri-iri da daidaikun jama’a da gidaje ke fuskanta a jihar Gombe sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi, musamman na kawar da tallafin man fetur.
Gwamnan ya yi kira ga jami’an raba kayayyakin da ‘yan sa kai da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana don tabbatar da gaskiya da inganci.
Gwamna Yahaya ya tabbatar wa al’ummar kasar cewa gwamnatin sa na kokarin kara samar da ayyukan yi ga al’umma domin bunkasa ci gaba da dakile kalubalen tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta.
Shugaban kwamitin kula da rabon kayan abinci na Jiha, Abdullahi Abdullahi ya baiwa Gwamnan tabbacin cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin tsoron Allah da kuma amfanin bil’adama.
Malam Abdullahi wanda kuma shi ne Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe, ya ce; “An kafa wasu kananan kwamitoci a matakin kananan hukumomi da unguwanni domin tabbatar da isar da kayayyakin ga marasa galihu a jihar.”
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Njodi ya bayyana cewa kaddamar da rabon kayan tallafin na daya daga cikin dimbin ayyukan da gwamnatin Gwamna Yahaya ta yi.
Saboda haka Farfesa Njodi,ya yi kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su yadda ya kamata, domin bunkasa noman amfanin gona da harkokin tattalin arziki.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply