Fira Ministan Vanuatu Ismael Kalsakau ya tsallake rijiya da baya, bayan da kuri’un ‘yan adawa yayi kasa da kuri’u 27 da ake bukata domin tsige shi.
Hakan ya biyo bayan sukar da aka yi wa Gwamnatinsa kan sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da Ostireliya.
Vanuatu, ta tsunduma cikin rikicin siyasa ne bayan da madugun ‘yan adawa Bob Loughman ya shigar da karar rashin amincewa, wanda kuma ya soki gwamnatin kasar kan karin mafi karancin albashi.
Kuri’u 26 na rashin amincewa da kudurin ya samu, idan aka kwatanta da kuri’u 23 na adawa da shi, amma ya kasa samun cikakkiyar rinjaye na 27 da ake bukata domin tsige firaminista a majalisar wakilai mai kujeru 52.
Kujera daya babu kowa sai dan majalisa daya bai halarci zaman ba saboda rashin lafiya.
A majalisar a ranar Laraba, Kalsakau ya ce zargin da ake yi masa ba shi da tushe balle makama, kuma shugabannin kasashen duniya sun kai ziyara cikin watanni takwas da suka gabata fiye da shekaru biyu na gwamnatin Loughman.
Kasar Sin ta kasance babbar mai ba da rancen ababen more rayuwa ga Vanuatu, inda ta ba da gudummawar ginin majalisar dokoki, da filayen wasanni da ofishin firaministan kasar, tare da gina tituna da magudanan ruwa.
Amurka da kawayenta na neman hana kasashen tsibiran Pasifik kulla huldar tsaro da birnin Beijing, bayan da China ta kulla yarjejeniyar tsaro da tsibirin Solomon.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply