A ranar Juma’a ne shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da gwamna Peter Mbah na jihar Enugu a fadar shugaban kasa dake Abuja.
‘Yan jarida sun tunkari Gwamnan a karshen taron amma ya ki cewa komai.
Sai dai ana sa ran tattaunawar tasa da shugaban ta tabo batun ci gaba da tsaro a jihar Enugu.
Gwamna Mbah a lokacin da ya hau kan karagar mulki ya bayyana ra’ayinsa na sauya fasalin Enugu daga bangaren gwamnati zuwa tattalin arziki mai zaman kansa ta hanyar zuba jari mai zaman kansa.
Karanta Haka: Gwamnan Jihar Enugu Ya Kara Rarrabu Da Dimokradiyya
A karo na karshe da gwamnan jihar Enugu ya ziyarci shugaban kasar, ya tattauna batun shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu da kuma sakin sa daga tsare.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply