Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Majalisu Sun Sha Alwashin Gina Mafi Kyau Na Najeriya

0 149

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya ta 10, Philip Agbese, ya ce majalisar ta himmatu sosai wajen gina Najeriya mai inganci da wadata.

 

Ya yi alkawarin ne a liyafar cin abincin dare da aka shirya don karrama sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, a Abuja.

 

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Ado/Okpokwu/ Ogbadibo na tarayya ya ce tuni shugabancin majalisar a karkashin kakakin majalisar Rt Hon Tajudeen Abbas ya sanya hannu a kai domin cimma wata manufa ta kasa.

 

Hon Agbese ya ce babban ajandar majalisar shi ne gudanar da budaddiyar majalisar da ta mai da hankali kan gaskiya da rikon amana.

 

Ya yi nuni da cewa majalisar ta mayar da hankali ne wajen ganin ta cika alkawarin da ta yi wa ‘yan Nijeriya daidaiku da kuma a dunkule a matsayin majalisa.

 

Ya jera ’yancin tattalin arziki, yanayin kasuwanci mai natsuwa, gudanar da al’amuran mulki, yancin kai, jarin zamantakewa, aminci, da tsaro, ilimi, da lafiya a matsayin jigon majalisar.

 

Ya kuma ce a dalilin haka ne shugabanni suka tsara wani shiri na tallafawa ‘yan kasa da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

 

Mataimakin kakakin ya kuma ce majalisar ta 10 tana duba hanyoyi da dama don inganta dokoki da kuma kusantar da mulki ga jama’a.

 

Daga cikin dabarun da aka yi la’akari da su, ya ce akwai amfani da fasaha da kuma tarukan da aka saba gudanarwa a cikin gari.

 

Ya ce akwai sabon salon kishin kasa, sadaukarwa, da sadaukar da kai ga al’amuran Nijeriya dangane da ‘yan majalisar wakilai ta 10.

 

Saboda da haka Hon Agbese ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna goyon bayansu ga majalisar a kokarinta na ganin an kyautata rayuwar kowa sannan kuma ya ba da tabbacin cewa nan da wani lokaci mai nisa Najeriya za ta fuskanci sabon salon rayuwa.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *