Akalla mutane biyu ne suka jikkata bayan wani bangare na wani jirgin saman Ukraine mara matuki da sojojin tsaron saman Rasha suka lalata ya fada kan wani gida a yankin Moscow, in ji gwamnan yankin.
Kusan jiragen sama 50 na ciki da wajen Babban Birnin Kasar sun samu cikas bayan da Rasha ta ce ta tare wani jirgin Ukraine mara matuki a gundumar Ruzsky da ke yammacin babban birnin kasar tare da lalata wani a gundumar Istrinsky da ke kusa.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha Rosaviatsia ta ce an hana masu shigowa da tashi daga manyan filayen jiragen sama hudu na Moscow, Vnukovo, Domodedovo, Sheremetyevo da Zhukovsky, lamarin da ya kawo cikas ga jiragen fasinja 45 da na jigilar kaya biyu.
Jami’an Rasha sun sha yin gargadin cewa jiragen yaki marasa matuka da ke shawagi a sararin samaniyar birnin Moscow tare da yankin da ke kewaye da ke da kusan mutane miliyan 22 na iya haifar da babban bala’i.
Hare-haren da jiragen yaki marasa matuka a cikin Rasha ya karu tun bayan da aka lalata jirage marasa matuka biyu a Kremlin a farkon watan Mayu.
Hare-haren da jiragen yaki marasa matuka a babban birnin kasar Rasha ya zama ruwan dare a ‘yan watannin nan.
Ba a dai san irin tasirin da hare-haren da jiragen yakin za su yi ba kan hasashe na yakin da ake yi tsakanin al’ummar Rasha.
A galibi dai Ukraine ba ta ce uffan kan wadanda ke kai hare-hare a yankin na Rasha ba, ko da yake Jami’ai sun bayyana gamsuwa a kansu.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply