Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani, ya ce matakin sakin fursunonin Amurka da ake tsare da su a arisa zai dauki tsawon watanni biyu, bayan wata yarjejeniya da Washington.
Kanaani ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin.
“Hukumomin da abin ya shafa sun sanar da wani takamaiman lokaci, kuma zai ɗauki tsawon watanni biyu kafin aiwatar da wannan aikin,” in ji Kanaani.
A farkon wannan watan, Tehran da Washington sun cimma yarjejeniya ta yadda za a ‘yantar da wasu Amurkawa biyar da ake tsare da su a Farisa yayin da za a saki dala biliyan 6 na kadarorin Iran da aka dakatar a Koriya ta Kudu.
REUTERS/Maimuna Kassim Tukur.
Leave a Reply