Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Dauko Hanyar Cika Alkawalin Da Ta Dauka A Bangaren Tsaro

Kamilu Lawal

0 232

Gwamnatin jihar Katsina ta kammala dukkanin shirye shirye domin horas da wasu dakaru na musamman da zasu taimakama jami’an tsaro wajen magance matsalar tsaro a yankunan jihar da matsalar tayi kamari

 

Kwamishinan ma’aikatar tsaro da lamurran cikin gida na jihar Katsina Hon. Nasiru mu’azu Danmusa ne ya bayyana haka ga taron manema labarai

 

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana matasan da za’a dauka zasu samu ingantaccen horo na yadda zasu gudanar da aikin tsare yankunan su, inda ya bayyana cewa kowane matashi daga cikin wadanda zasu karbi horon an zabo shi ne daga yankin da ya fito

 

Yace “bayan sun samu horon za’a tura kowannen su a yankin da ya fito domin su hadu tare da jami’an tsaro da nufin tunkarar matsalar  domin kawo karshenta,”

 

Nasiru Danmusa ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar ta amince da fitar da kudi domin tanadin kayan aikin da suka wajaba domin kaddamar da dakarun na cikin gida wadanda zasu yi aikin maido da tsaron da zaman lafiya a yankuna takwas da ke fama da matsalar tsaron a jihar ta Katsina

 

“Kuma mai girma gwamna ya aikewa majalisar dokokin jihar nan bukatar samar da doka da zata halasta kafa wata hukuma tare aiyukanta domin inganta ayyukan tsaro da zaman lafiyar al’ummar jihar.

 

“Daga cikin ayyukan hukumar wadda za’a wi lakabi da “Katsina State Community Watch Agency” akwai kula tare da horas da matasan da za’a dauka domin aikin tsaron yankunan da ake fama da matsalar tsaro a jihar,” inji Nasiru Danmusa.

 

 

Ya kara da cewa hakan wani bangare ne daga shirye shiryen da gwamnatin jihar keyi wajen kokarin ganin al’ummar jihar sun zauna lafiya domin cigaba da gudanar da harkokin tattalin arzikin su cikin kwanciyar hanlali, musamman sana’ar noma da kiwo dake zaman babbar hanyar da al’ummar jihar ke dogaro da ita

 

 

Idan dai za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirinta na kashe sama da naira  miliyan dubu bakwai wajen shiryen shiryen tunkarar matsalar tsaro domin kawo karshen ta a jihar

 

A wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Katsina fadar gwamnatin jihar, kwamishinan ma’aikatar tsaron da lamurran cikin gida Hon. Nasiru Danmusa yace majalisar zartaswar jihar ta amince da a kashe Naira biliyan bakwai da miliyan dari takwas da sha ukku da dubu dari hudu da ashirin da ukku da naira dari biyar da sittin domin sayen kayan aikin da za’a tunkari matsalar dasu da nufin kawo karshen ta a jihar

 

A yanzu haka ma dai majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da bukatar da gwamnan ya tura mata na kudurin samar da dokar domin kafa wata hukuma da zata lura da lamurran tsaro mai suna “Katsina State Community Watch Agency”

 

Ana sa ran idan gwamnan ya sanya hannu tare da kaddamar da hukumar zata taimakawa kudurin gwamnatin jihar wajen tunkarar matsalar tsaron tare da kawo karshenta a fadin jihar Katsina

 

 

Kamilu       Lawal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *