Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta bukaci Amurka da ta dakatar da sayar da“makamai” ga Taiwan, bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta amince da yiwuwar sayar da dala miliyan 500 ga tsibirin na binciken infrared da na’urori na jiragen sama na F-16, da kuma sauran kayan aiki.
Kakakin ma’aikatar Zhang Xiaogang ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, Sin tana kira ga bangaren Amurka da ya cika alkawarin da ya dauka na kin goyon bayan samun ‘yancin kai na Taiwan, da daina baiwa Taiwan makamai, da kuma dakatar da inganta huldar sojan Amurka a Taiwan.
REUTERS Ladan
Leave a Reply