Take a fresh look at your lifestyle.

Ukraine: An Kashe Mutane Hudu A Hare-Haren Rasha

0 150

Kimanin mutane uku suka mutu a wani hari da makami mai linzami da Rasha ta kai kan Ukraine cikin dare, sannan na hudu ya mutu a harin da aka kai, in ji jami’an Ukraine.

 

Ministan cikin gida Ihor Klymenko ya ce mutane ukun da aka kashe cikin dare ma’aikata ne a wata masana’antar da aka kai hari a yankin Poltava da ke tsakiyar kasar. Wasu 5 sun samu raunuka sannan ba a ji duriyar wani mutum ba.

 

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Andriy Yermak ya bayyana wurin a matsayin masana’antar mai da ke gundumar Myrhorod na yankin Poltava, ya kuma buga hotuna da ke nuna yadda kamfanin ke ci da wuta. Klymenko ya ce an kashe wutar.

 

“Mutanen suna aiki da dare,” in ji Yermak a cikin manhajar saƙon Telegram.

 

Oleksandr Prokudin, gwamnan yankin Kherson, ya ce an kashe wata mata mai shekaru 63 a harin da aka kai a kauyen Sadove da misalin karfe 10:40 na safe (0740 GMT) a ranar Litinin.

 

Rundunar sojin Ukraine ta ce Rasha ta harba makamai masu linzami guda hudu daga tekun Bahar Rum cikin dare, biyu daga cikinsu an harbo su.

 

Sojojin sun kuma ce yankin Kryvyi Rih da ke tsakiyar Ukraine an kai harin makami mai linzami. Hukumomin yankin sun ce an lalata gidaje masu zaman kansu da dama, amma ba a samu asarar rai ba.

 

Rasha wadda ta aike da dubun dubatan dakaru zuwa Ukraine watanni 18 da suka gabata, ba ta ce uffan ba kan rahotannin.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *