Take a fresh look at your lifestyle.

Babban Hafsan Sojin Sudan Yaje Kasar Masar A Tafiyar Farko Tunda Aka Fara Yaki

0 114

Jami’ai a Sudan sun ce babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bar kasar a wani jirgin sama zuwa Masar domin ganawa da shugaba Abdel Fattah al-Sisi.

 

Wannan dai shi ne karon farko da shugaban mulkin sojan Sudan ya fice daga kasar tun bayan barkewar rikici a can cikin watan Afrilu, tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF).

 

Shugaban Masar ya goyi bayan Janar Burhan a yakin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka ya tilastawa ‘yan Sudan fiye da miliyan hudu barin muhallansu.

 

Har zuwa ‘yan kwanaki kadan da suka gabata an tsare shugaban sojojin Sudan a cikin hedikwatar sojojin da ke birnin Khartoum.

 

Kasancewar a yanzu Janar Burhan ya samu damar barin kasar domin tattaunawa da abokinsa a Masar, wata alama ce da ke nuna cewa sojojin kasar ba su da wani matsin lamba.

 

Mai yiwuwa RSF mai hamayya da ita ta yi rauni a babban birnin kasar.

 

Amma a Darfur kungiyar RSF tana da karfi kuma tana kai hare-hare masu nasaba da kabilanci.

 

A ranar Litinin, Janar Burhan ya yi watsi da ra’ayin tattaunawar zaman lafiya tare da yin magana game da fatattakar ‘yan tawayen.

 

Da yawa daga cikin ‘yan Sudan da ke ganin ana ci gaba da lalata kasarsu, za su yi fatan cewa a bayan fage shugabannin yankin na yunƙurin sake yin wani yunƙuri na yin shawarwarin kawo ƙarshen yaƙin.

 

BBC/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *