Gwamna Roman Starovoit ya ce jiragen yakin Ukraine mara matuki guda biyu sun kai hari a garin Kurchatov na kasar Rasha, wanda ke da tashar makamashin nukiliya a yankin Kursk da sanyin safiyar Juma’a.
Ma’aikatan agajin gaggawa suna tantance barnar da wani ginin gudanarwa da kuma na mazaunin suka samu a harin, ya rubuta a cikin manhajar aika saƙon Telegram.
Starovoit bai ambaci wata illa da za ta iya yi wa tashar makamashin nukiliya ta Kursk ba ko kuma ya ba da cikakkun bayanai game da gine-ginen da aka yi niyya.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply