Take a fresh look at your lifestyle.

Gabon: Juyin Mulkin Sojoji Ya Kara Ta’azzara Rikici- Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

0 161

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce juyin mulki na kara ta’azzara rikici ne kawai, yana mai jaddada bukatar samar da dorewar shugabanci da bin doka da oda.

 

 

Guterres ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana jerin juyin mulkin da sojoji suka yi a nahiyar Afirka a wani taron manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

 

 

“Kasashe da yawa suna fuskantar ƙalubalen shugabanci. Amma gwamnatocin soja ba su ne mafita ba. Suna kara tsananta matsaloli. Ba za su iya magance rikici ba; za su iya kara dagula lamarin,” in ji Guterres.

 

 

A ranar Larabar da ta gabata ne sojojin suka mamaye kasar Gabon bayan juyin mulkin watan Yuli a Nijar, Burkina Faso a shekarar 2022, da Chadi, Guinea, Sudan da Mali a shekarun baya.

 

 

Gabaɗaya, duk juyin mulkin baya-bayan nan ban da Myanmar, a cikin 2021, an yi shi ne a ƙasar Afirka.

 

 

Sanarwar kwace iko da kasar Gabon ta zo ne jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben da ke cewa an sake zaben shugaban kasar Ali Bongo a karo na uku sakamakon wasu kura-kurai a rumfunan zabe.

 

 

Shugaban na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga dukkan kasashen da su gaggauta kafa cibiyoyin dimokiradiyya masu inganci da bin doka da oda.

 

 

Guterres ya bayyana bukatar karfafa kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar Tarayyar Afirka, a kokarinsu na diflomasiyya na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dimokuradiyya a nahiyar.

 

 

A sa’i daya kuma, ana bukatar samar da yanayi da zai bai wa ‘yan Afirka damar tunkarar matsalolin da ke haddasa tabarbarewar siyasa; rashin ci gaba shine babban al’amari, in ji shi.

 

 

“Ci gaba shine babban makasudi idan muna son samar da yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka,” in ji babban magatakardar, yayin da yake amsa tambayar da wani dan jarida ya yi masa.

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *