Sama da masu gadin gidan yari 50 da jami’an ‘yan sanda bakwai ne aka yi garkuwa da su a gidajen yari da dama a Ecuador, kamar yadda jami’ai suka ce.
Wasu bama-bamai na mota guda biyu kuma sun tashi a babban birnin kasar Quito, duka biyun sun nufi Hukumar kula da gidajen yari ta kasar (SNAI).
Babu wanda ya samu rauni a tashin bama-baman kuma an kama akalla mutane shida.
Hukumomin kasar sun yi imanin akalla daya daga cikin abubuwan da suka faru na iya zama ramuwar gayya ga ‘yan sandan neman makamai a daya daga cikin manyan gidajen yari na kasar.
Ministan cikin gida na Ecuador, Juan Zapata, ya ce Hukumomin na daukar mataki amma bai bayar da karin bayani ba.
“Mun damu da tsaron jami’an mu,” in ji Mista Zapata.
Sa’o’i kadan da suka gabata, wani bam ya nufi wani gini da SNAI ke amfani da shi a baya a Quito. Fashe na biyu ya nufi Hedikwatar Hukumar.
‘Yan sanda sun ce an kai harin ne daga baya ta hanyar amfani da wata mota da aka makare da bama-bamai.
Magajin garin Quito Pabel Munoz ya ce an kuma samu fashewar gurneti a cikin birnin a cikin dare.
Kasar Ecuador na fuskantar karuwar tashe-tashen hankula da ke da nasaba da kungiyoyin safarar miyagun kwayoyi, lamarin da ya kawo cikas ga tsarin gidajen yari da ba su da wadata da kuma cunkoso.
An kashe daruruwan fursunoni a wani kazamin fada da aka yi a gidajen yarin Ecuador da ke cunkoso a cikin ‘yan shekarun nan.
Shugaban Ecuador Guillermo Lasso ya ce “Matakin da muka dauka, musamman a tsarin gidan yari, sun haifar da tashin hankali daga kungiyoyin masu aikata laifuka da ke neman tsoratar da jihar.”
“Amma muna da tsayin daka kuma ba za mu koma kan manufar kama masu laifi ba, tarwatsa kungiyoyin masu aikata laifuka da kuma daidaita gidajen yarin kasar.”
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply