Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban ‘Yan Adawa A Senegal Ya Kawo Karshen Yajin Yunwa

0 81

Babbar jam’iyyar adawa a Senegal ta ce shugabanta, Ousmane Sonko ya kawo karshen yajin cin abinci da ya fara tun bayan kama shi a karshen watan Yuli.

 

Shugabannin musulmi sun bukace shi da ya kawo karshen yajin cin abinci.

 

An kwantar da shi a sashin kula da marasa lafiya a watan da ya gabata bayan rashin lafiyarsa ta tabarbare.

 

 

An tuhumi Mista Sonko, mai tsananin sukar shugaba Macky Sall da laifin tayar da kayar baya, da gurgunta harkokin tsaro da ayyukan ta’addanci.

 

 

Tuni dai aka dakatar da shi daga tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa bayan da wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda laifin lalata da wata budurwa.

 

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *