Take a fresh look at your lifestyle.

Musanya Kudi Zai Rage Dogara Akan Dala – Masanin Tattalin Arziki

0 105

Tsohon Darakta Janar na Cibiyar Kula da Kudade da Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma, WAIFEM Farfesa Akpan Ekpo ya bukaci babban bankin kasar CBN da ya dauki yarjejeniyar musayar kudi da bankin jama’ar kasar Sin, domin rage dogaro da daloli wajen ciniki.

 

“Wannan ne lokacin da za a aiwatar da musayar kudin Najeriya da China ta yadda ba za mu sanya ƙwayayen mu duka a cikin kwando ɗaya ba.

 

“Don haka ‘yan Najeriya da ke mu’amala da kasar Sin ya kamata su yi hulda da kudin kasar Sin ko da Naira ba da dala ko Yuro ba; wanda zai rage matsi akan dala ko fam.

 

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba yarjejeniyar musanya kudin da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai a shekarun baya, musamman ma ta fuskar karuwar farashin canji.

 

“Wannan shi ne lokacin da ya kamata a dauke shi da muhimmanci; Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar, an yi ta ne a takaice sannan ba mu sake sanin abin da ya faru ba.

 

“Idan aka yi la’akari da yanayin duniya, kasuwanni masu tasowa ta BRICS suna ƙoƙarin yin kasuwanci da kudaden kasashen biyu don rage mahimmancin dala, Yuro ko fam saboda waɗannan kudaden ba nasu ba ne kuma ba za su iya buga su ba.

 

“Don haka, idan har yanzu za mu iya aiwatar da musanya tsakanin Yuan-Naira na kasar Sin, zai taimaka sosai ga cinikayyar kasuwanci.”

 

 

LADAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *