Take a fresh look at your lifestyle.

Rasha ‘Da dabara’ ta janye daga Robotyne na Ukraine

0 133

Wani jami’in da Rasha ta nada ya ce Sojojin Moscow sun yi watsi da ƙauyen Robotyne na Ukraine, fiye da mako guda bayan Kyiv ya sanar da kwato shi.

 

Yevgeny Balitsky, babban Jami’in da Moscow ta girka a yankin Zaporizhzhia, ya fada a wata hira ta gidan talabijin cewa Sojojin Rasha sun janye saboda abin da ya kira dalilai na dabara.

 

 

“Rundunar sojojin Rasha sun yi watsi da shi, sun yi watsi da wannan matsuguni da dabara saboda kasancewa a kan wani wuri mara kyau lokacin da babu wata hanyar da za a iya tono gaba daya ba ma’ana ba ne. Don haka sojojin Rasha suka koma cikin tuddai,” wata kafar labarai ta RBC ta ruwaito.

 

A baya dai Rasha ba ta amince da asarar Robotyne ba, wanda Ukraine ta sanar da sake kama shi a ranar 28 ga watan Agusta.

 

A cikin bayananta na yau da kullun, ma’aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun dakile hare-haren Ukraine guda biyu a kusa da Robotyne.

 

Fiye da watanni 18 bayan mamayar Rasha, Ukraine ta ce tana samun galaba, kuma ta karya layin farko na katanga na Rasha a wurare da dama a fagen daga, duk da furucin da Moscow ta yi na cewa harin da Ukraine ta kwashe watanni uku ana yi bai yi nasara ba.

 

 

REUTERS\LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *