Take a fresh look at your lifestyle.

Koriya Ta Arewa za Ta ‘Dan-dana Kudarta’ Idan Ta Bai Wa Rasha Makamai-Amurka

0 123

Tattaunawar makamai tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa na ci gaba sosai, in ji wani jami’in Amurka, yana mai gargadin Kim Jong Un cewa kasarsa za ta biya farashi don baiwa Rasha makaman da za ta yi amfani da su a Ukraine.

 

Bayar da makamai ga Rasha “ba zai yi kyau a kan Koriya ta Arewa ba kuma za su dan-dana kudarsu da wannan a cikin al’ummomin duniya,” mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Amurka Jake Sullivan ya shaida wa manema labarai a fadar White House.

 

Fadar Kremlin ta ce a baya, ba ta da “abin da za a ce” game da sanarwar da jami’in Amurka ya yi cewa Kim ya shirya tafiya Rasha a wannan watan don ganawa da Shugaba Vladimir Putin da kuma tattauna batun samar da makamai zuwa Moscow.

 

Kim yana tsammanin za a ci gaba da tattaunawa game da makamai, in ji Sullivan, ciki har da matakin jagora da kuma .

 

Sullivan ya ce, “Mun ci gaba da murkushe sansanin masana’antar tsaron Rasha,” in ji Sullivan, kuma Masko yanzu “tana neman duk wani tushe da za su iya samu” don kayayyaki kamar harsasai.

 

Sullivan ya ce “Za mu ci gaba da yin kira ga Koriya ta Arewa da ta mutunta alkawuran da ta dauka na cewa ba za ta ba wa Rasha makaman da za su kashe ‘yan Ukraine ba.”

 

A ranar Litinin mai magana da yawun Majalisar Tsaron Amurka Adrienne Watson, ta ce Kim da Putin na iya shirin ganawa, kuma jaridar New York Times ta ruwaito wasu jami’an Amurka da kawayenta da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa Kim na shirin tafiya Rasha nan da mako mai zuwa domin ganawa da Putin.

 

Da aka tambaye shi ko zai iya tabbatar da tattaunawar, kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce: “A’a, ba zan iya ba. Babu abin da za a ce. “

 

 

 

REUTERS

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *