Tare da taimakon kaɗan daga hukumomi, mazauna ƙauyen ranar Lahadi sun dogara ga Allah kawai don ayyukan bincike da ceto.
Gawarwaki da dama da suka hada da Gawar ango da Amaryar shi da kanwar shi suna karkashin baraguzan ginin Hada, a cewar wani mazaunin garin . “Babu wanda zai tono gawarwakin. Muna rokonka da hukuma ta ji kukan mu. Muna neman a bude hanya.”
Bisa alkaluman hukuma da aka sabunta da yammacin ranar Lahadi, girgizar kasar ta kashe akalla mutane dubu biyu 2,122.
Girgizar kasar mai karfi ta shafe dukkan kauyukan da ke tsaunukan Atlas.
“Mutane sun shiga cikin rudani a nan, an ruguje kauyen Imine Tala gaba daya,” in ji wani mazaunin kauyen.
“Babu wanda zai taimaka. Dutsen ya fado musu. Har yanzu mutanen na karkashin baraguzan gine-gine kuma babu wanda zai iya kwashe duwatsun, kuma har yanzu hukumomi ba su aika da na’urorin da za a kwashe su ba, kwana uku kenan . Kuna iya jin warin gawawwakin ko’ina. Abin kunya ne hukumomi ba su taimaka wa wadannan mutane ba. “
A wasu sassan kasar kuma, kungiyar agaji ta Red Crescent ta Morocco da sojoji ne ke jagorantar aikin ceto.
Yammacin Imine Tale a Amziz, sauran wadanda suka tsira sun sami mafaka a cikin tantuna.
“A yankunan da ke cikin tsaunuka masu tsayi hanyar na da wahala, kuma muna fatan gwamnati da kungiyoyin fararen hula za su iya kai kayan agaji ga kauyukan da ke da wahalar isarsu saboda ba su da komai a wurin, don haka da yardar Allah za su samu tallafi. ,” in ji Mostafa Ushun.
Baya ga kasar Sipaniya, Maroko ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa ta karbi tallafi daga kasashen Birtaniya, Qatar, da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kasar da ta fi karfi a Arewacin Afirka ta yi barna sama da 2,400.
Girgizar kasar ta ranar Juma’a ta afku a nisan kilomita 72 (mil 45) kudu maso yammacin cibiyar ‘yan yawon bude ido ta Marrakesh, inda ta shafe daukacin kauyukan da ke tsaunukan Atlas.
A ranar Lahadin da ta gabata girgizar kasa mai karfin awo 4.5 ta afku a wannan yanki.
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply