Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Za Ta Halarci Taron G77 A Kasar Kuba

0 86

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima na kan hanyarsa ta zuwa birnin Havana Cuba, domin wakilcin shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin kasashen G77+ na kasar Sin, wanda ake gudanarwa daga ranar 15 zuwa 17 ga Satumba, 2023.

 

 

Zai bi sahun sauran shugabannin duniya da suka hada da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres a wajen taron, domin tattaunawa kan batutuwan ci gaban da mambobin kungiyar ke fuskanta, musamman daga kudancin duniya.

 

 

Taron dai zai binciko hanyoyin da za a bi wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta wajen ci gaban kasashe mambobin kungiyar da ke amfani da kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire don bunkasa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

 

 

Har ila yau, mataimakin shugaban kasa Shettima, zai kasance a gefen taron kasashen biyu, da sauran shugabannin kasashen duniya, domin inganta huldar kasuwanci da zuba jari a Nijeriya, bisa tsarin raya tattalin arziki na gwamnatin shugaba Tinubu.

 

Shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel ne ya karbi bakuncin taron na Havana a matsayinsa na shugaban G77 da Sin.

 

 

Taken taron kolin na bana shi ne: “Kalubalen ci gaban da ake fuskanta a halin yanzu: rawar da kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ke yi.”

 

 

Najeriya dai kasa ce ta kafa kungiyar G77 wadda kasashe masu tasowa saba’in da bakwai suka kafa a shekarar 1964.

 

 

Ƙungiyar – haɗin gwiwar kasashe masu tasowa 134 tare da kashi 80% na yawan jama’ar duniya, na nufin inganta manufofin tattalin arziki na mambobin kungiyar da kuma samar da ingantaccen damar yin shawarwari tare a Majalisar Dinkin Duniya.

 

 

Mataimakin shugaban kasar yana tare da ministan noma da raya karkara, Abubakar Kyari; Ministan kirkire-kirkire, kimiya da fasaha, Uche Nnaji, da babban sakataren ma’aikatar harkokin waje, Amb. Adamu Lamuwa, da sauransu.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *