Take a fresh look at your lifestyle.

Hatsarin Jirgin Ruwa: Kakakin Majalisa Abbas Yayi Alhinin Wadanda Abin Ya Shafa

0 109

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana bakin cikin shi kan hadurran da kwale-kwalen da yake afkuwa a kasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

 

 

Da yake mayar da martani na musamman kan abubuwan da suka faru a jihohin Adamawa da Neija, shugaban majalisar ya yi kira da a hada karfi da karfe da gwamnati da ma’aikatan jirgin ruwa domin kare rayuka da dukiyoyi a kogunan Najeriya.

 

 

Shugaban majalisar ya yi Allah wadai da irin halin da harkar sufurin ruwa ke ciki a madadin hanya da jirgin kasa na zirga-zirgar jama’a da kayayyaki, a yanzu ke ta tafka kura-kurai.

 

 

Shugaban majalisar Abbas yace yana kira ga hukumomin da abin ya shafa da su yi la’akari da sake duba ka’idojin aiki tare da neman tsauraran matakan kiyaye lafiyar ma’aikatan jirgin da fasinjoji.

 

 

Yayin da yake addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu Shugaban majalisar, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, da jama’a, da gwamnatin jihohin Neja da Adamawa kan wannan lamari da ya faru.

 

 

A daren Juma’ar da ta gabata, an ce mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin ruwa ya kife a tafkin Njuwa, kauyen Rugange a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.

 

 

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 100 a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja ya kife, inda fasinjoji 30 suka mutu.

 

 

A ranar Litinin kuma, an samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale a garin Kwatan Mallam Adamu, da ke kauyen Gurin, a karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, inda ya halaka mutane sama da 10.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *