Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Yaba Wa Gwamnatin Kano

Yusuf Bala Nayaya, Kano/

0 27

Ministan lafiya a Najeriya Farfesa Muhammad Ali Pate da tawagar wasu wakilai da suka hadar da na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da wasu kungiyoyi na kasa da kasa suka kai ziyara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin Kano a kokarin inganta harkokin lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

 

 

A yayin ziyarar wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dr.Walter Kazadi Mulombo ya yaba wa gwamnatin ta Kano kan kokarin da ta yi a yaki da cutar Polio da cutar Mashako ta Diptheria da cutar Maleriya wanda a cewarsa ya kamata sauran jihohi su yi koyi da jihar ta Kano.

 

 

“Jihar Kano ta ciri tuta wajen farfado da shirin kula da lafiya a matakin farko, dama abin da ke zama tarnaki shine aga gwamnati na aiki da gaske kan kula da lafiya, wannan gwamnati kuwa ta Kano shine abin da take yi. Wannan dai ya kasance abin zabirarwa kan matakan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke bi na dakile cututtuka tun daga tushe.” A cewar Dakta Kazadi.

 

 

Har ila yau Dakta Kazadi ya ce “Kano ta zama inda cutar Mashako ta Diphtheria tafi yawa amma mun gani a zahiri babban misali yadda gwamnati ta himmatu wajen dakile cutar. Muna fatan sauran jihohi za su yi koyi da ita”

 

 

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yaba wa wannan tawaga bisa jagorancin na Ministan lafiya Muhamad Ali Pate da yace sun zo a lokacin da ya dace da gwamnatin ta sa himma kan harkoki na kula da lafiyar al’ummarta a gaba.

 

 

“Bara na nuna godiya kan kulawar da kuka nuna wa al’ummar Kano ganin ta kasance a gaba cikin jihohi da kuka zaba kan wannan ziyara. Ina yabawa da abokan huldarmu ta samar da ci gaba musamman a yaki da muke da cutar HIV da tarin TB da cutar Maleriya da sauran cutittika.”

 

 

Gwamnan bayan yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma bukaci kungiyoyin na kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa jihar ta Kano a yayin da take ba wa fannin kula da al’ummarta fifiko.

 

 

Yusuf Bala Nayaya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.