Take a fresh look at your lifestyle.

MAJALISAR WAKILAI TAYI KIRA GA HUKUMOMIN TATTARA HARAJI DA SU DAI-DAI TA ALKALUMAN SU

0 162

Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kudi ya shawarci hukumomi a bangaren man fetur da su daidaita alkaluman da aka fitar a fannin.

Mataimakin shugaban kwamitin, Rep. Saidu Abdullahi ne ya bayar da wannan shawarar a lokacin da mahukuntan babban hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa, a wajen taron 2023-2025 na matsakaita na kashe kudade da dabarun kasafin kudi tare da ma’aikatu da hukumomi a Abuja.

 

Ya ce duk hukumomin da ke wannan fanni suna nuna alkaluma daban-daban da kuma rudar da ‘yan Najeriya.

 

Ya ce: “Rikicin alkaluma ya kasance babban kalubale a Najeriya. Ba ma ganin hadin kai tsakanin hukumomi daban-daban a bangaren.”

 

 

Da yake mayar da martani ga wasu daga cikin tambayoyin, babban daraktan kula da harkokin man fetur na kasa, Mista Abiodun Adeniji, ya ce hukumar ta kasance sabuwa kuma tana kokarin daidaita kanta.

 

 

An dage halartar da hukumar gidan waya ta ne saboda gaza cika sharuddan kwamitin. An ce su sake bayyana ranar Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *