Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Mali Ta Soke Bukin Ranar ‘Yancin Kai Bayan Hare-Hare

0 93

Gwamnatin mulkin sojan Mali ta soke bukukuwan da aka shirya yi na zagayowar ranar samun ‘yancin kai a ranar 22 ga watan Satumba.

 

Sanarwar ta biyo bayan taron wata majalisar ministoci ne.

 

A bara, shugaban mulkin sojan Guinea ya halarci faretin sojoji da aka shirya domin bukukuwan cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai a Mali.

 

A yayin zaman majalisar ministocin na ranar Laraba, shugaban sojojin Mali ya umarci gwamnati da ta ware kudaden da aka shirya don bukukuwan bana domin taimakawa wadanda hare-haren baya-bayan nan ya rutsa da su da kuma iyalansu.

 

Sanarwar ranar ‘yancin kai ta zo daidai da sabunta ayyukan soji da ‘yan awaren Abzinawa ke yi, da kuma wasu hare-hare da ake dangantawa da ta’addanci.

 

A ranar Talata ne kungiyoyin ‘yan awaren Abzinawa dauke da makamai suka kaddamar da farmaki kan sansanonin sojojin da ke garin Bourem, wanda sojojin suka ce sun dakile.

 

Bangarorin biyu sun bayar da rahotanni masu cin karo da juna na abubuwan da suka faru, amma dukkansu sun ba da rahoton mutuwar mutane da dama.

 

Wani harin da aka kai kan wani jirgin ruwa na fasinja a kogin Neja, wanda ake zargin ‘yan ta’adda, ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a makon jiya.

 

Wadannan al’amura dai na faruwa ne a karkashin ci gaba da janyewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD zuwa kasar Mali.

 

Kasar Mali ta fada cikin rudani a shekarar 2012 bayan da ‘yan aware da ‘yan ta’adda suka barke a arewacin kasar.

 

Goita ya bayyana “bacin ran shi” game da asarar da aka yi sakamakon “hare-haren wuce gona da iri kan jirgin ruwa (da kuma) hare-haren da aka kai kan sansanonin da ke garuruwan Bamba, Gao da Bourem”, in ji majalisar ministocin.

 

Wannan dai shi ne jawabin shi na farko a bainar jama’a kan harin da aka kai ga jirgin ruwan.

 

 

Africanews/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *