Masar ta Lallasa Najeriya Kuma Ta Samu Nasarar Lashe Gasar Olympics
Maimuna Kassim Tukur,Abuja.
‘Yan wasan Masar Omar Assar da Dina Meshref sun doke ‘yan wasan Najeriya biyu Olajide Omotayo da Olufunke Oshonaike da ci 3-1 (11-8, 6-11, 11-1, 12-10) inda suka lashe gasar cin kofin Afrika karo na 26 na ITTF. Wannan ya tabbatar da tikitin Nahiyar zuwa gasar Olympics ta Paris 2024 a Faransa.
Wannan ne karo na biyu da Masarawa suka yi nasara a kan abokan hamayyarsu yayin da su ma suka doke ‘yan Najeriyar zuwa tikitin shiga gasar Olympics a ranar Laraba 13 ga Satumba, 2023.
https://von.gov.ng/egypt-defeats-nigeria-secures-mixed-doubles-olympic-spot/
Sakamakon haka, Masarawa za su tafi birnin Paris domin wakiltar Afirka a gasar ta maza da mata, da kuma gasar cin kofin kasashen biyu.
Kara karantawa: Kwallon Tennis din tebur: Najeriya ta kasa samun tikitin shiga gasar Olympics na Paris
Da wannan ci gaban, Masar ta samu dukkan tikitin shiga gasar Olympics ta Paris 2024 a kan babbar matsala a gasar ITTF ta Afirka karo na 26 a Tunis.
Sai dai hakan ya hana Oshonaike na Najeriya damar kafa sabon tarihi a matsayin dan wasan Najeriya na farko da dan Afirka da kuma dan wasan kwallon tebur na takwas da ya taka rawa a gasar Olympics.
Maimuna Kassim Tukur.