Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano, Dakta Muhammad Mahmud ya ce kimanin yara 520 ne ake zargin sun rasa rayukansu sakamakon bullar cutar Mashako a jihar a wannan shekara ta 2023.
KU KARANTA KUMA: Diphtheria: Kungiyar agaji ta Red Cross ta ba da gudummawar kayayyakin masarufi a jihar Kano
Mahmud ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wani taron wayar da kai na kwana daya da manema labarai suka yi kan bullar cutar amai da gudawa, wanda asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya tallafa a Kano ranar Talata.
“Akwai bayanan da muka samar ta hanyar sa ido na dijital da tsarin bayar da rahoto. A bana Kano ta ba da rahoton mutane kusan 8,700 da ake zargin sun kamu da cutar Mashako, sannan 6,300 aka tabbatar suka kamu, kuma ake zargin kimanin yara 520 ne suka mutu sakamakon wannan rashin lafiya.
“Mun bi diddigin hakan a kullum da mako-mako, mun yi imanin cewa rahotannin sun fi abin da muke samu, yayin da muke shaida karuwar lamarin daga watan Yuli,” in ji shi.
Shugaban ya kara da cewa an samu rahoton kararrakin ne daga kananan hukumomi 39 daga cikin kananan hukumomi 44 da ke jihar, yayin da kararrakin suka kara ta’azzara a cikin kananan hukumomi takwas. Ya ce a cikin makon nan UNICEF ta kai alluran rigakafi miliyan 1.2 ga gwamnatin jihar Kano a ci gaba da tallafa wa gwamnati domin magance bullar cutar Mashako.
A nasa jawabin, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ya ce akasarin wadanda ake zargin sun kamu da cutar amai da gudawa yara ne da ba a yi musu allurar rigakafi ko daya daga cututtukan da ke kashe yaran da suka hada da diphtheria ba.
“Ya zuwa yanzu, an samu rahoton bullar cutar Mashako mafi yawa daga jihar Kano. Misali, a cikin kananan hukumomi 44 na jihar Kano cutar ta yadu zuwa kananan hukumomi 39.
“Tun daga watan Janairun 2023, jihar Kano ta ba da rahoton bullar cutar Mashako sama da 5,800 a jihar. Ko da yake an sami raguwa a cikin rahoton da aka bayar a watan Yuni, har zuwa watan Yuli, waɗannan cututtukan Mashako suka karu. Ya zuwa makon da ya gabata sama da mutane 400 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar mutane 11 a jihar Kano,” inji shi.
A cewar shi, kananan hukumomi takwas ne cutar ta fi shafa: Ungogo (2651), Dala (989), Fagge (943), Gwale (714), Kumbotso (713), Nassarawa (538), Kano Municipal (506) da Tarauni. (269).
Ladan Nasidi.
Leave a Reply