Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin kasar ta sanar da mutuwan daya daga cikin yayanta kana wakilin gidan Rediyon Muryar Najeriya (VON) a jihar, Alhaji Hamisu danjibga kwanaki uku bayan bacewarsa.
An dai tsince gawar marigayin ne a wani rami na soakway dake kusa da gidansa sakamakon wari da yan islamiyya suka ji yana tashi da ba a saba jin irinsa ba, inda daliban makarantar suka ankaras da Malamansu. Lamarin da yasa aka gano gawar marigayin bayan da iyalai da yan uwa da kuma abokanin arziki suka tabbatar da haka a jiya laraba ashirin ga watan satumbar nan da muke ciki.
Tuni dai a ka yi jana’izar marigayin a Gusau babban birnin jihar Zamfara kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
NUJ reshen jihar Zamfara ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalai da kuma gidan rediyon muryar Najeriya bisa wannan rashi, ta kumma bayyana kaduwarta dangane da kisar gillar da yan ta’adda suka yi wa marigayin tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da binciken kwakwaf domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika ta yadda za su fuskanci hukuncin da ya dace da su.
Tuni dai shugaban sashen Hausa na Muryar Najeriya Tukur Garba Arab ya bayyana kisan marigayin a matsayin tsantsar rashin imani kuma ya taba zukatan ma’aikatan mu don haka wannan rashi ne ga daukacin ma’aikatan kafafeen yada labarai ba ga gidan Rediyon Muryar Najeriya ba kadai, duba da yadda marigayin ke sadaukar da kai wajen hidimtawa aikin ta fuskar amfani da kwarewarsa.
“Muna cikin alhini tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalai da yan uwansa, Allah ya jikan Hamisu Danjibga”. In ji Tukur Arab.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply