Take a fresh look at your lifestyle.

Harin Jirgin Rasha Ya Raunata Mutum Daya Da Lallata Tashar Jiragen ruwa – Ukraine

2 163

Mace guda ta jikkata tare da lalata gine-gine da ababen more rayuwa na tashar jiragen ruwa a harin makami mai linzami da Rasha ta kai cikin dare a tashar jiragen ruwa na Odesa da ke Kudancin Ukraine, in ji rundunar sojin Ukraine a ranar Litinin.

 

“An kai mummunar hari a Tashar ruwa na teku a Odesa, gobara ta tashi a otal din tashar, wanda ba’a anfani da shi na tsawon shekaru ,” in ji Hukumar Kudancin Ukraine ta hanyar aika saƙon Telegram.

 

“Ma’aikatan kashe gobara sun kawar da shi nan da nan.”

 

Rundunar sojin sama ta Ukraine ta ce na’urorin tsaronta na sama sun lalata jiragen sama marasa matuka 19 da Iran ta kera Shahed, da makami mai linzami 11 da makami mai linzami guda biyu da Rasha ta harba a kan Ukraine cikin dare, akasarin su a Odesa.

 

An lalata wasu jirage marasa matuka uku a ranar Lahadin da ta gabata, in ji sanarwar.

 

Tun da farko, gwamnan yankin Odesa, Oleh Kiper, ya ce an kai wata mata asibiti bayan da ta samu rauni sakamakon tashin bam din.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

2 responses to “Harin Jirgin Rasha Ya Raunata Mutum Daya Da Lallata Tashar Jiragen ruwa – Ukraine”

  1. I have been exploring for a bit for any high quality articles or blog posts in this kind of house . Exploring in Yahoo I eventually stumbled upon this site. Studying this information So i’m glad to exhibit that I’ve a very excellent uncanny feeling I discovered exactly what I needed. I so much unquestionably will make sure to don?t fail to remember this site and provides it a look regularly.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *