Take a fresh look at your lifestyle.

GWAMNAN JIHAR KEBBI YA RUSA MAJALISAR ZARTARWA

0 314

Gwamnan jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya, Atiku Bagudu ya amince da rusa majalisar zartarwa ta jihar Kebbi daga ranar Laraba 7 ga Satumba, 2022.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Babale Umar Yauri a Birnin Kebbi.

Gwamnan ya yaba da gudunmawar daidaiku da kowane memba na majalisar ministocin ya bayar tare da gode musu bisa sadaukarwar da suka yi wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar a tsawon lokacin da suke rike da mukamai.

Ya kuma yabawa daukacin ‘yan majalisar da aka rusa bisa yadda suka gudanar da ayyukansu yayin da nan ba da dadewa ba za a sanar da sabuwar majalisar zartarwa ta jiha.

Sanarwar ta nuna cewa za a iya sake nada wasu daga cikin mambobin majalisar da aka rusa da kuma wasu daga waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *