Take a fresh look at your lifestyle.

HUKUMAR NAICOM, JIHAR KATSINA TA KADDAMAR DA KWAMITIN GUDANAR DA SHIGA INSHORA

0 88

Hukumar Inshora ta kasa da gwamnatin jihar Katsina sun kaddamar da wani kwamiti da zai gaggauta bin diddigin yadda ake aiwatar da inshorar dole a fadin jihar.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Hon. Kwamishinan kasuwanci na jihar Alh. Muktar Gidado Abdulkadir tare da mataimakin shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Katsina Mal. Mustapha Mohammed Sirajo.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan NAICOM, Ofishin SSG, Ofishin Shugaban Ma’aikata a Jiha, Ma’aikatar Kudi, Ma’aikatar Lafiya da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu ne suka halarci bikin kaddamar da kwamitin fasaha kan wayar da kan jama’a da aiwatar da inshorar dole da Takaful a jihar.

Gwamna Aminu Masari a lokacin da yake kaddamar da kwamatin fasaha ya bayyana cewa shirin samar da inshorar Takaful abin farin ciki ne kuma zai zama madadinsa musamman don jawo hankulan al’ummar jihar da suka bar baya da kura saboda matsalolin addini ko al’adu.

Ya kuma tabbatar wa da hukumar inshorar gwamnatin jihar Katsina cikakken goyon bayan ci gaban inshorar a jihar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.