Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Sandan Indiya Sun Karyata Labarin Harin Da Aka Kai Gidan Babban Minister

0 191

‘Yan sandan Indiya sun yi watsi da rahotannin “karya da yaudara” cewa wasu gungun ‘yan zanga-zanga sun kai hari a wani gida mai zaman kansa na Biren Singh, Babban Ministan Jihar Manipur na Arewa maso Gabas, ya kara da cewa “yana da cikakken tsaro”.

 

Kalaman na ranar Alhamis sun biyo bayan rahotannin kafafen yada labarai ciki har da na Reuters, yayin da zanga-zangar ta afku a babban birnin jihar Imphal, wanda ya raunata fiye da mutane 80, kafin dawowar zaman lafiya a ranar Juma’a.

 

 

“Labarin da aka yi wa gidan babban ministar karya ne kuma yaudara ce,” in ji ‘yan sandan jihar a dandalin sada zumunta na X, wanda a da ake kira Twitter. “An riga an samar da isasshen tsaro.”

 

 

Rikicin kabilanci ya jefa jihar da ke kan iyaka da Myanmar cikin abin da masana harkokin tsaro da dama suka bayyana a matsayin yakin basasa da aka gwabza kan filaye da ayyuka da kuma siyasa tsakanin al’ummar Meitei da ke da rinjaye da kuma tsirarun kabilun Kuki.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *