Rasuwar Sarauniyar Ingila ke da wuya, sai mulkin ya koma kan ɗanta magajinta Charles, tsohon Yariman Wales, ba tare da wani bikin naɗin sarauta ba.bayan jira na shekaru 70 , Amma akwai matakai na al’adu da dama da za a aiwatar masa kafin a tabbatar da shi.
Za a dinga kiransa da Sarki Charles na III.
Wannan ne mataki na farko na zama sabon sarki. Zai iya zaɓa daga cikin sunayensa huɗu – Charles Philip Arthur George.
Ba shi ne kaɗai wanda ke samun sauyin suna ba.
Duk da cewa shi ma mai gadon sarautar ne, Yarima William ba zai zamo Yariman Wales kai tsaye ba. Sai dai, tuni ya karɓi ɗaya tsohuwar sarautar mahaifin nasa ta Duke na Cornwall.
Ita kuma matarsa Catherine za a dinga kiranta da Duchess ta Cornwall.
Matar Charles kuwa, sabon sunanta shi ne Sarauniya Consort – consort ce kalmar da ake amfani da ita wajen kiran matar sarkin da ke kan mulki
Leave a Reply